Iyayen Trump sun turashi makarantar soji tun yana ɗan shekara 13 kafin daga bisani ya kammala karatun digirinsa a fannin tsimi da tanadi wato Economics a jami’ar Pennsylvania.
Bayan ƙarɓar bashin dala miliyan 1 da yayi daga wurin mahaifinsa a shekarar 1970, Trump ya samar da katafaran ginin Trump Tower da kuma ofisoshi da gidaje masu ɗauke da sunansa.
Trump ya ƙware a ƙulla harkokin kasuwanci amma ya gamu da tafka asara da gaza biyan bashin banki da kuma gamuwa da tazgaro a kasuwancinsa.
Daga shekarar 2003 an ƙara sanin shugaba Trump sakamakon bayyana da yake yi a wasu shirye-shiryen talabijin da suka haɗa da The Apperentice da kuma Celebrity Apprentice.
A shekarar 2005 Donald Trump ya auri matarsa Melania Knauss wadda za ta sake shiga fadar White House tare da mijin nata bayan shan rantsuwar kama aiki a yau.
Anjima kaɗan ne za a rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka a karo na biyu, a wata nasara mai ban mamaki da ya samu cikin wani yanayin zazzafar adawar siyasa a ƙasar.
Zai karɓi rantsuwar kama aiki a hannun alƙalin-alƙalai na Amurka John Roberts da ƙarfe 12 na rana agogon Amurka, wanda ya zo dai dai da ƙarfe 5 agogon GMT.
Shugaba mai barin gado Joe Biden zai miƙa mulki ga Donald Trump a wannan taro na yau, kuma bayan karbar rantsuwar kama aiki Trump zai yi jawabi ga ƴan ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI