Barkanmu da wannan lokaci a cikin shirinmu da muke sharhi akan al’amurran yau da kullum. Kasar Isra’ial ta sake bayyana irin cin zarafin da take yiwa Falasdinawa a Gaza, Kudus da Zirrin Gaza.
A wannan makon mun sake kasancewa tare da Ferfesa Murat Yesiltas, Daraktan Harkokin Tsaro a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam wato SETA……
Isra’ila na kokarin sake yin wani zagaye, musamman game da hare-hare kan Gaza, inda daruruwan fararen hula suka rasa rayukansu tare da jikkata dubbai. Wannan zagayen ya dogara ne da dabarun yin rufa-rufan mamayar Falasdinawa da dukkan illolinta da kuma rage tasirin Gaza. Tun daga ranar da aka kafa kasar Isra’ila, za a iya bayyana abubuwa da yawa dangane da dalilan “kirkirarrun halaccin” da Isra’ila ta dogara da su kan mamayar Falasdinu mataki-mataki a cikin munanan manufofin da ta aiwatar. Daga cikin wadannan abubuwan akwai uku da ke kan gaba.
Lamari na farko, shi ne yadda ta fa’idantu da kisan kare dangin da aka yi wa Yahudawa (Holocost) a lokacin yakin duniya na biyu. Bayan kisan kare dangin da Jamus ta yiwa Yahudawa an mayar da kyamar yahudawa a matsayin haramtaccen lamari kuma an dauki matakan wayar da kai, musamman a tsakanin kasashen Turai domin hana sake faruwar irin lamarin. Isra’ila ta yi amfani da wacanan damar na yaki da kyamar yahudawa wajen gudanar da wasu tsarukan da ta halastawa kanta. Hakan ya baiwa gwmanatin Tel Aviv damar bayyana duk irin sukar da aka yi wa Isra’ila akan ayyukanta na kin kari a Falasdin a matsayar ra’ayin kyamar Yahudawa.
Wani abin mamaki shi ne, yadda Isra’ila ta mayar da wanan lamari na yaki da kyamar Yahuwa siyasa da kuma yadda Amurka da kasashen Turai suka dauki shi da muhinmanci. Da farko ma shugabanin kasashen wadanan kasashen ke bayyana irin wannan ra’ayin wanda shugabannin Isra’ila suka koya, lamarin da ya sanya duk wani matakin kin karin da Isra’ila ta yi a Falasdin ba za’a iya cewa uffan akansa ba.
Lamari na biyu da ya sanya Isra’ila ci gaba da aikata ayyukan kin kari tare da cin karanta ba babbaka a kasar Falasdinawa shi ne yadda ta zama ‘yan lelen kasar Amurka ta hanyar yin faada da neman taimako. Kasar Isra’ila wacce ta samu amincewar Amurka mintuna 11 bayan an kafa ta; kawo yanzu ma ta na ci gaba da samun goyon bayan kasar Amurka. Taimakon soja na Amurka ya fara ne a hankali a matakin farko; an bayar da ita ne bisa ka'idar "fifikon sojan Isra'ila a yankin" bayan shekarar 1967, a lokacin da aka fahimci cewa ba za a sami wani babban martani daga kasashen yankin ba.
Bayan cin zaben Joe Biden an yi tsanmanin za’a samu sauyi akan irin muhimmiyar gudunmowar da Amurka ke baiwa Isra’ila. A yayin yakin neman zabe, Biden ya yi alkawarin bayar da gudunmowa ga tsaron Isra’ila kamar kuma yadda ya yi alkawarin bayar da gudunmowa a tsaron kasa da kasa da kare hakkokin bil adama. Sai dai, irin salon da mulkin Biden ya nuna tun lokacin da Isra’ila ta fara kai farmakai na nuni ga rashin iya samar da sauyi ga Falasdinu bayan mulkin Trump.
Abu na uku, wanda ke share fage ga abin da Isra’ila ke yi; kuma mai tasiri ga irin manufofin mamayar Falasdinu da take yi, yana da alaka da daidaiton yankin da kuma yadda kasashen yankin masu karfi suke da ra’ayoyi daban-daban yadda suka kasance suna fafutukan cimma burinsu ne kawai. Wannan lamarin ya kasance mai tasiri tun farkon rikicin Isra’ila-Falasdin har izuwa lokacin yakin Isra’ila da Larabawa har ma ya zuwa yanzu. Sabili da rashin hadin kan kasashen yankin da sabanin manufofi da ra’ayoyin dake tsakaninsu ne ya baiwa Isra’ila damar mamaya kasar Falasdinawa baki daya.
Daidaiton yankin dai ya yiwa Isra’ila daidai musanman a cikin shekaru 10 da suka gabata. Bugu da kari, hakan bai ma sanya Isra’ila ta kashe wasu makudan kudade ba. Isra’ila, bayan kifar da gwamnatin Husni Mubarak a Misira, wacce ta damu game da yiwuwar tabarbarewar yarjejeniyar Camp David da aka yi tsakanin shugaban Masar, Anwar Sadat da Firayim Ministan Isra’ila Menachem Begin a ranar 17 ga Satumba 1978; ta sami kwanciyar hankali bayan juyin mulkin shekarar 2013 a Masar da kuma afkuwar tsananin yakin basasa a Syria.
Sauyi a dukkan ko ma daya daga cikin wadannan abubuwa uku da suka daure wa Israila gindi zai shafi matakai na gaba da Isra’ila za ta ɗauka a Falasɗinu.
Wanan sharhin Ferfesa Murat Yesiltas ne Daraktar Harkokin Tsaro a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayyar Dan Adam wato SETA..dake nan Ankara babban birnin kasar Turkiyya. Ku huta Lafiya..