Har zuwa safiyar yau Litinin masu aikin kashe gobarar na ci gaba da ƙorafi kan yadda ƙaƙƙarfar iskar da suka bayyana da mai haɗarin gaske ke ci gaba da daƙile ƙoƙarinsu na shawo kan wutar dajin wadda ta faro ci tun a daren Lahadi wayewar garin Litinin ɗin makon jiya, kuma kawo yanzu ta haddasa gagarumar ɓarna a wani yanayi da masana ke ganin ta na ci gaba da sauri fiye da hasashe ganin yadda kawo yanzu ta fantsama hatta yankunan da a baya basa cikin haɗarin fuskantar irin wannan ibtila’i.
Dubban gidaje ne yanzu haka suka zama toka a Los Angeles inda masu kashe gobara ke cewa aikin da suke na komawa baya duk da tallafin da suke samu daga tawagar Injiniyoyi da ke aikin katse dukkanin na’urorin da ka iya ingizawa ko kuma ta’azzara wutar dajin.
Wutar dajin ta Carlifonia ta ci gaba da ƙarfafuwa zuwa gabashi inda ta tunƙari cibiyar adana kayan tarihi ta Getty Arts da kuma wata ta daban da ta tunƙari yammaci wadda ita kuma ke barazana fitaccen kwarin San Fernando mai yawan jama’a.
A cewar Deanne Criswell shugabar sashen kai ɗaukin gaggawa a Amurka, yanayin ƙarfin iskar ka iya tunzura yanayin ƙarfin wutar zuwa mil 50 a sa’a guda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI