Masana sun bayyana cewa guguwar ta Milton ba ta yi barnar da aka yi hasashen za ta yi a wasu sassa na jihar ta Florida ba, bayan da tun farko aka fargabar za ta haddasa gagarumar matsala kwatankwacin makamanciyarta ta Helene makwanni 2 da suka gabata.
Bayanai na nuna cewa zai ɗauki makwanni ko watanni gabanin kammala gyare-gyaren ɓarnar da guguwar ta yi ga tarin gidajen jama’a.
Yanzu haka dai Amurkawa fiye da miliyan 3 ne ke rayuwa a gidajen tafi da gidanka na wucin gadi da mahukunta suka samar musu bayan da ibtila’in ya tilasta musu rabuwa da matsugunansu.
Guguwar ta Milton wadda aka bayyana a matsayin ta 5 mafi ƙarfi, ƙiyasin da ƙwararru suka yi na nuna cewa Amurka za ta kashe aƙalla dala biliyan 100 wajen gyara ɓarnar da ta haddasa.
Tuni dai ibtila’in annobar ya juye zuwa siyasa bayan da ɗan takarar shugabancin ƙasar kuma tsohon shugaba Donald Trump ke zargin jam’iyyar Democrat da sakaci wajen kai ɗauki ga waɗanda ibtila’in ya shafa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI