Kasa mafi mafa da talauci na nahiyar Amurka watau Haiti mai al’umma miliyan 11 ta fuskanci annobar guguwa a yayinda da take fama da kwayar cutar COVID-19.
A yayinda ake hasashen Corona zata yi kamari a kasar a watan Yuni sai gashi kasar kuma ta fuskanci annobar guiguwar hurricane da ake ganin zata kai har a watan Nuwamba.
A guguwar da aka yi a kasar a baya sun lalata da yawan sassan kasar inda Guguwar Matthew a shekarar 2016 ta lalata da yawan kudancin kasar.
Masu hasashe a jami’ar Jihar Colorada sun bayyana cewa a shekarar 2020 za’a samu guguwar akai-akai fiye da na wadandad suka gabata wadanada daga cikin 16 zasu kasance mahaukatar iska sabili da sauyin yanayi.