A yau shugabannin ƙasashe ke jawabi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 79

A yau shugabannin ƙasashe ke jawabi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 79

Babban Magatakardar Majalisar Antonio Guterres ne zai jagoranci biki buɗe taron, wanda shi ne karo na 79, yayin da Philemon Yong ɗan ƙasar Kamaru zai ci gaba da jagorantar taron tun daga farko har zuwa ƙarshe.

An dai bayyana cewa shugabannin ƙasashe da na gwamnatoci 133, da mataimakan shugabannin ƙasashe 3, da ministoci akalla 45 ne ke wakiltar ƙasashensu a taron, kuma kamar yadda aka tsara, shugaban ƙasar Brazil, da na Amurka da kuma na Turkiya na daga ciin waɗanda za su gabatar da jawabai a wannan talata.

Ko baya ga manyan matsaloli na tattalin arziki da kuma sauyin yanayi da ake fama da su a duniya, hare-haren Isra’ila akan yankin Palasdinu waɗanda a yanzu ta ƙara faɗaɗa su zuwa kudancin Libanan, da rikicin Rasha da kuma Ukraine, su ne za su fi kasancewa muhimman batutuwa a wannan karo.

Tun gabannin fara taron ne Babban Magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi gargaɗi a game da illolin wannan yaƙi da kuma yadda zai iya rikita yankin Gabas ta Tsakiya baki dayansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)