An bayyana watan Yuli a matsayin watan da aka fi yin zafi da ya haura digiri 0.93 na matsakaicin zafi a karni na 21 a fadin duniya.
Dangane da bayanan da Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa (NOAA) ta fitar, yanayin zafi na watan Yuli a arewacin duniya ya karya rikod na tsawon shekaru 142, inda matsakaicin zafin watan ya haura digiri 1.54.
A watan Yuli, Asiya ta fuskanci watan da ya fi zafi a rikod, yayin da zafin Yuli a Turai ya kasa kadan da na watan Yulin shekarar 2018 amma ya kasance na biyu.
Rick Spinrad, darektan hukumar kula da yanayin teku da yanayi ta kasa, ya ce watan Yuli yawanci watan da ya fi zafi ne a shekara.
"Amma wannan rikod din ya kasance ɗaya daga cikin alamun dake haifar da damuwa akan sauyin yanayi a kasa da kasa."
Hukumar kula da yanayin teku ta kasa ta lura cewa rahotannin ta na wata-wata na nuni da sauye-sauyen da aka dade ana yi a cikin rahoton Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi (IPCC) wanda aka fitar a makon da ya gabata.
A cikin rahoton IPCC, an yi gargadin cewa za a wuce mataki 2 na dumamar yanayi a karni na 21 idan ba a dauki mataki ba.