
A wata hira da aka yi da Trump, ya ce suna son ɗaukar wannan matakin ne don ganin mayaƙan Hamas ba su sake koma wa yankin ba.
Na ƙuduri aniyar mallake yankin Gaza ta hanyar siyeshi, idan muka sake gina shi, za mu iya ba wa wasu ƙasashen Gabas ta Tsakiya suma damar gina wasu sassansa haka nan wasu mutane ma za su iya samun damar ta hannunmu. Amma mun ƙuduri aniyar kwace yanki da kuma tabbatar da cewa Hamas ba za ta koma cikinsa ba.
Shugaban na Amurka ya kuma ce ƙofarsa a buɗe take don tattauna yiwuwar kwashe wasu Falasɗinawa zuwa Amurka, sai dai ya ce za a yi hakan ne bisa ga wasu ka'idoji.
Waɗan nan kalamai na Trump dai sun fuskanci suka daga ƙungiyar Hamas, inda a wata sanarwar da ta fitar ta hannun Ezzat El Rashq, ta ce Gaza ba ta sayarwa bace wani ɓangare ne na ƙasar Falasɗinawa, kuma ba za su yarda da shirin kwashesu daga yankin ba.
Kafin kalaman na Trump dai, anji shugaban Isra’ila Isaac Herzog, na cewa shugaban na Amurka zai gana da takwarorinsa na Masar Abdel Fattah el-Sisi da Sarki Abdullah na Jordan da kuma Yarima mai jiran gado na Saudiya Modammed bin Salman, duk da dai bai sanar da abin da tattaunawar za ta kunsa ko kuma ranar da za a gudanar da ita ba.
A makon daya gabata ne dai Trump, ya fara gabatar da buƙatar kwashe Falasɗinawa daga yankin na Gaza don mallakawa Amurka yankin, matakin da ya fuskanci suka daga ƙasashe da ƙungiyoyi da dama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI