A-shabaab ta kai tagwayen hari a Somaliya

A-shabaab ta kai tagwayen hari a Somaliya

Kungiyar ta'addar Al-shabaab ta kai tagwayen hari a sansanonin sojoji biyu dake kasar Somaliya.

A harin da aka kai a sansani soja mai nisan kilomita 100 daga Mogadishu babban birnin Somaliya ba'a bayyana ko an samu hasarar rayuka ko raunanan mutane ba.

A ranr 25 ga watan Maris ma kungiyar Al-shabaab ta kai hari a ma'aikatun Majalisar Dinkin Duniya da na Tarayyar Afrika dake Mogadishu.

A wancan harin mutum 3 sun rasa rayukansu inda kuma wasu biyar suka raunana.

 


News Source:   ()