Guguwar Ivo ta afkawa yankunan da tuni ke fama da ambaliya daga guguwar Eowyn da Herminia.
Hukumar kula da yanayi ta kasar Faransa ta yi gargadin cewa lamarin na iya yin muni a cikin kwanaki masu zuwa abin da ya sanya ma hukumomin da abun ya shafa cikin Shirin ko ta kwana.
Garin na Redon, wanda koguna biyu ke kewaye da shi, ya kasance cikin ambaliya tun a ranar Laraba, abin da ake ganin ya shafi mazauna yankin kusan 750.
Kungiyar agaji ta Red Cross ta kafa sansanin bayar da mafaka ga mutane 50 a wani dakin motsa jiki na yankin da aka warewa mutum 200.
Haka zalika birnin Rennes shima yana cikin yanayin dimuwar aukuwar ambaliya mafi muni da aka gani tun bayan shekaru 40 da suka gabata, abin da ya tilastawa hukumomi kwashe mutum 200 ya zuwa yanzu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI