Rohitash Kumar, matashi dan shekara 25 da ke fama da matsalar magana da ji, ya kamu da rashin lafiya kuma an kai shi asibitin Jhunjhunu da ke Rajasthan (arewa).
Kafofin yada labarai na India sun ruwaito cewa ya yi fama da ciwon farfadiya, kuma likita ne ya tabbatar da mutuwarsa da isar shi asibiti.
Birnin Bénarès (Varanasi),a kasar India © Peter Adams/Getty imagesAmma babban likitan asibitin, D. Singh, ya shaida wa AFP cewa wani likita ya "shirya rahoton mutuwar mutane ba tare da gudanar da binciken gawarwakin ba, sannan aka aika da gawar don kona ta".
Babban likitan ya kara da cewa "ba da jimawa ba" da isar da gawar wurin da ake kone su ,aka gano cewa "jiki ya fara motsawa" yana numfashi".
An kai matashin asibiti a karo na biyu, amma an tabbatar da mutuwarsa a jiya Juma’a.
Wasu daga cikin shugabanin Hindu a India © Côme Bastin/RFIAn dakatar da likitoci uku, kuma ‘yan sanda sun kaddamar da bincike, kamar yadda Times of India da wasu kafafen yada labarai na India suka ruwaito.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI