A cikin shekarar bana an kaiwa Musulmi hari sau 188 a Jamus

A cikin shekarar bana an kaiwa Musulmi hari sau 188 a Jamus

Ma’aikatar cikin gidan Jamus ta sanar da cewa hukumar ‘yan sanadan kasar ta tabbatar da cewa a cikin wannan shekarar an kai hare-haren kalubalantar Islama har sau 188 a fadin kasar.

Daga cikin hare-haren an kaiwa akallan Masallatai 15 hari tsakanin Afirilu zuwa Yunin 2020, haka kuma gomman Musulmi an jikkatasu ko tozartasu a wasu hare-haren da aka gudanar akan titunan kasar. Musulmi tara ne dai aka jikkata a wasu hare-haren kuma.

A yayinda aka gabatar da kara akan ire-iren wadanan hare-haren na kalubalantar Islama  kawo yanzu dai ba’a kama kowa ba.

Haka kuma an tabbatar da cewa an aikata laifukan kalubalantar Musulmi a birnin kasar Berlin har guda 40.

 


News Source:   ()