A ƙarshe dai Biden ya cika alƙawarin kai ziyara Afirka kafin ya bar mulki

A ƙarshe dai Biden ya cika alƙawarin kai ziyara Afirka kafin ya bar mulki

Tashar layin dogon wanda Amurka ke ɗaukar nauyin wani bangare na aikin da wani bashi da ta ciyo, ya haɗa ƙasashen jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da Zambia zuwa tashar jirgin ruwan Angola ta Lobito da ke kan tekun Atlanta, wadda ke bada damar shige da ficen kayayyaki cikin sauƙi zuwa yammacin duniya.

Hakan kuma na bada damar fitar da albarkatun da suka haɗa da jan ƙarfe da ma’adanin Cobalt, da ake samarwa a Congo, kuma su ne manyan sinadarai da ake amfani da su wajen haɗa batira da sauran kayayyakin masu amfani da lantarki.

China dai ita ce babbar ƙasar da ke taka rawar gani a harkokin ma’adinan Congo, al’amarin da ke tayarwa da Amurka hankali.

A watan Satumbar da ya gabata ne, China ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da ƙasashen Tanzania da Zambia, da za ta bada damar gina tashar layin dogo a yankin gabashin Afrika.

Yayin da Biden ke kai ziyarar aikin a Angola  a Litinin ɗinnan, kwanaki kaɗan kenan kafin ya bar shugabancin Amurka, ana sa ran sabon shugaba Donald Trump da zai kama aiki a watan Janairu, zai yi kusanci da Angola wajen tabbatar da kammala aikin, a cewar wasu jami’ai biyu da suka yi aiki da Trump zamanin mulkinsa na farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)