Ofishin da ke kula da ayyukan jinƙai na Majalisar ɗinkin duniya OCHA ya ce aƙalla jami’an agaji da ke aikin kai ɗauki yankunan da ke fama da rikici 333 ne aka kashe cikin shekarar nan mafi ƙololuwa da aka taɓa gani a tari cikin shekara guda.
Kakakin hukumar ta OCHA Jens Laerke yayin jawabinsa a Geneva ya bayyana cewa a yankin gabas ta tsakiya kaɗai Isra’ila ta kashe jami’an jinƙan da yawansu ya kai 281 adadin da ya zarta na yawan jami’an jinƙan da aka kashe a bara na jumullar mutum 280 a dukkanin sassan duniya.
A cewar jami’in ko kaɗan ɓangarorin da ke rikici da juna basa bayar da kariya ga jami’an agaji yayinda a wasu wuraren ake kashe su da gangan bisa sanin cewa jami’ai ne da ke kai ɗauki ga waɗanda rikici ya rutsa da su ko kuma suka samu raunuka ko suke cikin wani yanayi na buƙatar abinci.
Laerk ya nanata cewa jami’an agaji a ilahirin sassan da ke fama da rikici na fuskantar barazana inda a wurare irin Gaza da Sudan da Lebanon da Ukraine ake ci gaba da kisan su ba ƙaƙƙautawa inda a jumlace adadin jami’an agajin sauran ƙungiyoyi da ba na Majalisar ɗinkin duniya ba kimanin 268 suka mutu a fagen daga a ƙoƙarin tallafawa mutanen da suka raunata ciki har da ƴan ƙasashen ƙetare 13.
Baya ga jami’an majalisar ɗinkin duniya OCHA ta ce sauran jami’an da Isra’ila ta kashe a Gaza akwai jami’an Red Cross da kuma na Red Crescent.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI