Tun shekara ta 2005 aka dage yanke hukuncin kisa a kasar da ke kudancin Afirka ko da yake kotuna na ci gaba da zartar da hukuncin, musamman kan laifukan da suka danganci aikata kisan kai da cin amanar kasa da ta'addanci.
Dokar kawar da hukuncin kisa, ta ce kotuna ba za su iya yanke hukuncin kisa ba kan kowane laifi kuma duk wani hukuncin kisa da ake yi zai bukaci a mayar da shi zaman gidan yari.
Akalla mutane 59 ke karkashin hukuncin kisa a Zimbabwe a karshen 2023, in ji Amnesty International a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta yi maraba da wannan sabuwar doka da ta bayyana a matsayin wani lokaci mai tarihi.
Kasashe 24 da ke yankin kudu da hamadar Sahara sun soke hukuncin kisa kan duk wani laifi yayin da wasu karin kasashe biyu suka soke shi.
Mnangagwa ya kasance mai adawa da hukuncin kisa tun bayan da aka yanke masa hukuncin kisa a shekarun 1960 saboda tarwatsa jirgin kasa a yakin neman 'yancin kai, ko da yake daga bisani an sassauta hukuncin a wancan lokaci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI