Zazzaɓin shawara na cigaba da sanadiyar rashin rayuka a Najeriya

Zazzaɓin shawara na cigaba da sanadiyar rashin rayuka a Najeriya

An bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu a kasar Najerıya dake Afirka ta Yamma sakamakon cutar zazzabin shawara ta kai 95.

Daraktan Cibiyar Kula da Yaduwar Cuttutuka ta Kasar Najeriya watau (NCDC) reshen jihar Bauchi Dkt. Rilwanu Muhammed ya bayyana cewa a cikin mako daya mutum 8 sun rasa rayukansu sanadiyar kamuwa da cutar zazzabin shawara.

A bisa haka daga watan Satumba kawo yanzu a fadin kasar Najeriya annobar ta yi sanadiyar rayuka 95.

Muhammed, ya kara da cewa "A makon jiya yayain da muke yawon kanfen din yin allurar riga-kafin shawara mun samu labarin rasuwar mutum 8, bincike ya nuna cewa shawarar ce ta yi ajalinsu"

Muhammed, ya bayyana cewa an fara daukar matakan kauda cutar inda ya kara da kira ga al'ummma da suka rinka tsabtace muhalli.

A fadin kasar Najeriya a bara annobar shawarar ta yi sanadiyar rayukan mutum fiye da 300.

Gwamnatin kasar na ci gaba da yaki da cutar da ta kaddamar tun daga ranar 12 ga watan Satumbar shekarar 2017.

 


News Source:   ()