Zazzabin Lassa ya yi ajalin mutane 63 a jia Ondo da ke Najeriya

Zazzabin Lassa ya yi ajalin mutane 63 a jia Ondo da ke Najeriya

A watanni 4 da suka gabata mutane 63 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Zazzabin Lassa a jihar Ondo da ke kudancin Najeriya.

Shugaban Kungiyar Likitoci ta Najeriya Reshen Jihar Ondo Wale Oke ya fadi cewar a tsakanin watan Afrilu da Yuli a yankunan jihar daban-daban mutane 482 ne suka kamu da Zazzabin Lassa inda daga ciki 63 suka rasa rayukansu.

Oke ya kara da cewar cutar Lassa ta fi Corona kashe mutane a jihar inda ya kara da cewar gwamnati ta fara bayar da magunguna kyauta don yaki da cutar.

A lokacin bazarar kowacce shekara a tsakanin watannin Mayu da Nuwamba Zazzabin Lassa na bulla a Najeriya inda a shekarar 2019 mutane 129 suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar a Najeriya.

Cutar Zazzabin Lassa ta bulla a karon farko a Najeriya a shekarar 1969 a jihar Borno, kuma baya ga kasar, a kasashen Mali, Togo, Gana, Laberiya da Saliyo ma an samu bullar cutar.

Ana daukar cutar daga kashin bera, a saboda haka mahukunta suke gargadar jama'a da su kula da tsafta sosai.


News Source:   ()