Mutane 216 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Lassa da ake dauka daga dabbobi a Najeriya.
Sanarwar da Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Kasa ta Najeriya (NCDC) ta fitar ta ce a jihohi 27 da suka hada da Edo, Ebonyi, Bauchi da kuma Babban Birnin Kasar Abuja an samu mutane dubu 1,036 dauke da cutar Zazzabin Lassa.
Sanarwar ta ce daga farkon shekara uwa yanzu mutane 216 cutar ta kashe a Najeriya.
A shekarar da ta gabata cutar ta yi ajalin mutane 129 a Najeriya.
A duk lokacin bazara tsakanin watannin Nuwamba da Mayu ana samun bullar cutar Lassa a Najeriya.
Cutar Lassa da ta bulla a kasashen Afirka da suka hada da Mali, Togo, Gana, Laberiya da Saliyo, ta bulla a Najeriya a karon farko a shekarar 1969 a jihar Borno da ke arewa maso-gabashin kasar.
Gwamnatin Najeriya ta aiyana dokar ta baci a kasar game da cutar Lassa da ake dauka daga kashin bera.