An sanar da cewa a cikin mako guda mutum 23 suka rasa rayukansu sakamakon zazzabin cizon sauro bayan fara damina a kasar Mali.
Kafafen yada labaran cikin gidan kasar Mali ne suka rawaito cewa a arewacin kasar a makon jiya an samu mutum dubu 13 da zazzabin cizon sauro ya kwantar.
A cikin makon jiyan zazzabin cizon sauron ya yi sanadiyar rayukan mutum 23, daga farkon shekara kawo yanzu kuma mutum 59 ne suka rigamu gidan gaskiya sakamakon kamuwa da zazzabin cizon sauron a arewacin kasar ta Mali.
Ma'aikatan kiwon lafiya na sharhin cewa sanadiyar karkata kudaden magance zazzabin cizon sauron zuwa wajen yaki da Covid-19 da aka yi ne ya kara gurbata lamarin yaki da zazzabin cizon sauron a fadin kasar.
An dai lura da cewa zazzabin cizon sauron na karuwa ne lokacin damina sabili da ruwan sama dake taruwa a gurare da dama lamarin dake haifar da haifafan sauraye.