Mau zanga-zanga na fadar cewa "Isra'ila mai laifi!" ko Yancin kasar Labanon, da kuma rera wakoki.
Rahotanni na bayyana cewa masu zanga-zanga kusan dari suka yi tattakin kimanin kilomita 1.5 a birnin na Dakar.
An bayana kasancewa wasu yan kasar ta Lebanon a Senegal a wannan tattaki.
Har ila yau masu zanga-zangar na dauke da alamomin yin Allah wadai da farmakin da Isra'ila ke kaiwa Gaza. Zaher Zeidna mai magana da yawun masu zanga-zangar ya ce: "Ba za mu iya zama cikin damuwa ba game da radadin wadanda a kullum suke ganin ana wargaza kasarsu.
Birnin Dakar na kasar Senegal © JOHN WESSELS / AFPYa kara da cewa "Yakin da ake yi a Lebanon da Gaza bala'i ne da ba za a iya kwatanta shi ba, kisan kiyashi ne.
" Yakin da ake gwabzawa a Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023 ya bazu zuwa kasar Lebanon, inda Isra'ila ta kaddamar da farmaki ta kasa a kudancin kasar a ranar 30 ga watan Satumba, tare da samun goyon bayan jiragen sama, kan kungiyar Hezbollah mai goyon bayan Iran.
Masu goyon bayan yan Falasdinu AFP - JUSTIN TALLISIsra'ila ta ce tana son kawar da kungiyar Hezbollah da ke kawance da Hamas na Falasdinu a yankunan da ke kusa da kan iyakar Isra'ila tare da ba da damar komawa arewacin yankinta na mazauna kusan 60,000, wadanda suka raba da muhallansu na tsawon shekara guda.
Akalla mutane 1,418 ne aka kashe a kasar Lebanon tun bayan fara kai hare-haren wuce gona da iri kan kungiyar Hezbollah a ranar 23 ga watan Satumba, a cewar alkaluman da kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayar bisa bayanan hukuma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI