Zanga-zangar adawa da Rwanda ta barke a Jamhuriyar Dimokardiyyar Congo

Zanga-zangar adawa da Rwanda ta barke a Jamhuriyar Dimokardiyyar Congo

An nuna yadda fusatattun mutane dauke da tutar Congo, ke kona tayoyi da kuma rufe hanyoyi a babban birnin kasar, wanda ke da dubban tazarar kilomita tsakaninsa da Goma.

Jamhuriyar Congo hadi da gwamnatocin wasu kasashen dai, na zargin cewa akwai sojojin Rwanda da ke taimawa ‘yan tgawayen M23 wajen kwace ikon yankuna da dama na kasar.

M23 ta kwace ikon Goma na dan gajeren lokaci a shekarar 2012, inda suka gaza samun galaba kan dakarun gwamnati a wancan lokaci, amma a shekarar 2022 mayakan kungiyar suka sake bazama a fagen daga.

Mazauna Goma, sun ce sun jiyo amon harbin bindiga cikin dare a birnin mai dauke da mutane miliyan biyu, bayan da kungiyar ta ce ta kwace ikonsa a ranar Litinin.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an jiyo amon fashewa da kuma harbin bindiga kusa da filin jirgin saman Goma da gwamnati ta rufe.

Shugaba Paul Kagame na Rwanda, ya wallafa a shafinsa na X cewa, ya amince da batun tsagaita wuta a tattaunawarsa ta wayar tarho da sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, amma be bayyana cewa ko zai janye sojojin kasarsa daga birnin na Goma ba.

Goma dai wani yanki ne da ake huldar kasuwanci sosai, wanda kuma ke dauke da dubun dubatar daga cikin ‘yan gudun hijira miliyan shida da rikici ya tilastawa barin muhallansu a gabashin Jamhuriyar Congo.

Har yanzu dai babu cikakken bayani, kan karfin ikon da M23 ke da shi akan Goma da kuma adadin wuraren da ta mamaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)