Sakataren Baitulmalin ƙasar Felix Nkulukusa ne ya bayyana matakin da ya ce, ta asusun kamfanin samar da wutar lantarkin ƙasar Zesco aka tura ƙudin, wanda ya bayyana a matsayin koma baya mai ban takaici a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsalolin tattalin arziki.
Da yake magana a birnin Lusaka, Nkulukusa ya bayyana cewa, an aika da kusan dala miliyan 80 daga wannan asusu bisa kuskure, lamarin da ke kara dagula al'amura a kasar ta Zambia.
Ƙasar Chinan ce ta gina kamfanin samar da lantarkin a matsayin bashi, amma sai aka fara biyan kudin bisa kuskure, yayin da ake ci gabata da nazari kan basussukan tsakanin ƙasashen biyu.
A watan Yunin bara , Zambia ta amince da masu ba da lamuni na ƙasashen waje don sake fasalin basussukan da ake bin ƙasar na dala biliyan 6.3 ciki harda dala biliyan 4.1 da China ke bin ƙasar, domin duba yiwuwar yafe mata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI