Zambiya ta ayyana kwanaki 21 na juyayi da zaman makoki akan rasuwar shugaban da ya kafa kasar Kenneth Kaunda.
A cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, an sanar da cewa za a saukar da tutocin kasa-kasa sannan an ayyana kwanaki 21 na zaman makoki na kasa ga "Baban da ya kafa kasar"" Kaunda.
A cikin sanarwar, an bayyana cewa Kaunda ya mutu cikin kwanciyar hankali da karfe 14:30 agogon gida a asibitin sojoji inda yake karbar magani tun ranar Litini.
Shima shugaban kasar Zambiya Edgar Chagwa Lungu ya gabatar da sanarwa a sakon ta'aziyar sa, wanda ya yada a shafin sa na Twitter, inda yake cewa "Ina yi wa dangin Kaunda ta'aziyya yayin bakin cikin mutuwar wani fitaccen dan Afirka.
Kaunda, wanda ya mulki kasar tsawon shekaru 27 tun daga 1964, lokacin da Zambiya ta sami 'yancin kanta daga hannun Biritaniya, an san shi da lakanin "KK", kamar yadda al'umman kasar ke kiransa.
Ana yi wa Kaunda lakabi da "Gandhi na Afirka" saboda gwagwarmayarsa ta rashin jituwa da Turawan mulkin mallaka na Birtaniya.
Kaunda, wanda ya hau mulki a matsayin Shugaban Kasa bayan samun ‘yancin kasar, ya fadi a zaben farko na jam’iyyu da yawa a shekarar 1991 sannan ya mika mulki ga Fredrick Chiluba.
Kaunda ya kasance daya daga cikin jiga-jigai a gwagwarmaya da gwamnatocin fararen fata marasa rinjaye na lokacin a kasashen Afirka ta Kudu.
Kaunda, wanda ya sake dawo da martabar siyasa a bayan mulkin shugaban kasa, ya gudanar da ayyukan yaki da cutar kanjamau da kuma sasanta tsakanin kasashen duniya a wannan lokacin.