Za a yi wa 'yan Afirka allurar riga-kafin da lokacin amfani da ita ya wuce

Za a yi wa 'yan Afirka allurar riga-kafin da lokacin amfani da ita ya wuce

A kasashen Afirka 13 an amince a yi wa jama'a allurar riga-kafin da lokacin amfani da su ya wuce.

An bayyana cewa, alluran riga-kafin Corona na da karin watanni 3 na rayuwa bayan lokacinsu na asali, a saboda haka za a iya amfani da su ga jama'a.

Rubutacciyar sanarwar da Hukumar Yaki da Cututtuka ta Afirka (Africa CDC) ta fitar ta ce, a tsakiyar watan Mayu an aika da alluran riga-kafi na Oxford/AstraZeneca guda dubu 925 zuwa kasashen Afirka 13 wadanda aka rubuta 13 ga Afrilu ne ranar karshe ta amfani da su ta karshe.

Wasu daga cikin kasashen da aka bawa kyautar alluran ne suka bayyana damuwarsu game da wucewar lokacin amfani da alluran riga-kafin.

 


News Source:   ()