A kasar Saliyo dake yammacin Afirka an shirya soke hukuncin kisa.
Mataimakin Ministan Shari'a Umaru Napoleon Koroma ya sanar da cewa, gwamnati ta fara aiyukan soke yanke hukuncin kisa a kasar.
Koroma ya kuma ce, Majalisar Ministocin Shugaban Kasar Saliyo Julius Maada Bio ta dauki matakin soke hukuncin kisa don kare hakkokin 'yan kasar.
Koroma ya kara da cewa, tun shekarar 1998 ba a sake zartar da hukuncin kisa a Saliyo ba, kuma an saukaka kusan dukkan hukuncin kisa da aka yanke.
Koroma ya kara da cewa, gwamnati ta mikawa majalisar dokoki kudirin soke hukuncin kisan, kuma da zarar ta amince batun zai zama ya zo karshe.