Kamfanin dillancin labaran Nijar, ANP, ya ce ministan ya faɗi hakan ne a lokacin da ya ke ba da bayanai game da ma’aikatarsa a birnin Yamai.
"Ƙasarmu na da faɗi sosai, kuma mun bai wa hukumar sufurin jiragen sama ANAC umarnin saussauta wasu dokoki domin taimakawa wajen samar da waɗannan kamfanonin. Saboda haka, ANAC ta fitar da sharuɗɗan samun damar wucewa ta sararin samaniya da sauri da kuma damar sauka a ƙasar," in ji ministan.
Ya kuma bayyana cewa an sauƙaƙa hanyoyin samun takardun shaidar ayyukan jiragen sama a ƙasar.
Kazalika kamfanin dillancin labaran Nijar ya ambato ministan yana cewa an riga an kafa kwamiti domin gaggauta bayar da takardun da ake buƙata wajen samar da waɗannan kamfanonin.
Ministan ya ce wannan aikin , "wani ɓangare ne daga cikin dabarun buɗe ƙasar ga duniya domin ƙarfafa hanyoyin da suka haɗa Nijar da makwabtanta da kuma sauƙaƙa sufuri a cikin ƙasar."
Ministan ya ƙara da cewa, "yana da muhimmanci a samu ƙwararrun ma’aikata da kuma kayayyakin aiki wajen aiwatar da wannan aiki kuma mun yi sa’a saboda muna da wannan ƙarewar."
“Kafa kamfanin jiragen saman tarayyar AES na cikin abubuwan da muka saka a gaba,” in ji ministan yana mai ci gaba da cewa “wannan aikin na ci gaba cikin sauri kuma insha Allahu nan ba da jimawa ba za mu samu wani kamfani mai kalan AES wanda zai haɗa manyan biranenmu tare da wasu wurare ".
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI