Za a gudanar da zaɓen sabon shugaban bankin AFDB a Abidjan a watan Mayu

Za a gudanar da zaɓen sabon shugaban bankin AFDB a Abidjan a watan Mayu

'Yan takara biyu sun fito daga Afirka ta Yamma: Tsohon Ministan Tattalin Arziki na Senegal (2019-2022), Amadou Hott, da na Mauritania (2008-2015), Sidi Ould Tah.

Wasu biyu kuma sun fito ne daga Kudancin Afirka: masanin tattalin arzikin Zambia Samuel Munzele Maimbo da Bajabulile Swazi Tshabalala na Afirka ta Kudu, wanda shi ne mataimakin shugaban cibiyar.

Ɗan takara na karshe shi ne tsohon gwamnan bankin tsakiyar Afrika (2017-2024), ɗan ƙasar Chadi Abbas Mahamat Tolli.

Bankin AfDB, wanda aka kafa a shekarar 1964, yana da ƙasashe membobi 81, ciki har da ƙasashen Afirka 54.

Shugaban Bankin Raya Afirka Dr. Akinwumi Adeshina. Watan Nuwambar 2022 Shugaban Bankin Raya Afirka Dr. Akinwumi Adeshina. Watan Nuwambar 2022 © REUTERS/Emilie Madi

Yana daya daga cikin manyan bankunan ci gaban ƙasashe daban-daban kuma albarkatunsa suna zuwa musamman daga biyan kuɗi na kasashe membobinsu, lamuni da ake bayarwa a kasuwannin duniya, da biyan lamuni da samun kuɗin shiga.

Yana taimaka wa kasashen Afirka ta hanyar inganta zuba jari a fannoni daban-daban kamar masana'antun noma, sufuri, makamashi da kiwon lafiya.

Tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari da Akinwumi Adeshina bayan samun nasarar zama shugaban Bankin Raya Ƙasashen Afirka Tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari da Akinwumi Adeshina bayan samun nasarar zama shugaban Bankin Raya Ƙasashen Afirka Bashir

Adewoumi Adesina ya sauka ne a matsayin shugaban cibiyar bayan wa'adin shekaru biyu na shekara biyar inda asusun bankin na AfDB ya ninka fiye da ninki biyu zuwa kusan dala biliyan 200.

An sake zaɓen shi a shekarar 2020, a matsayin ɗan takara ɗaya tilo, duk da zargin rashin gudanar da mulki da son zuciya. Kwamitin kwararru ne suka wanke shi jim kadan kafin hakan.

Kwamitin Gwamnoni ne ke zabar Shugaban na AfDB, wanda ya kunshi wakilan kasashe membobi 81, wadanda yawanci ministocin kudi da tsare-tsare ne ko kuma gwamnonin manyan bankunan kasar.

A ranar 29 ga watan Mayu ne za a gudanar da zaɓen a Abidjan, hedƙwatar hukumar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)