Shugaban Kasar Aljeriya Abdulmajid Tebbun ya bayyana rushe majalisar dokokin kasar don a gudanar da zabe da wuri, kuma cikin awanni 48 zai yi sauye-sauye a majalisar zartarwarsa.
Bayan kammala kwanciya a asibiti a Jamus tare da dawowa kasarsa, Tebbun ya gana da shugabannin jam'iyyu inda ya matsa lamba kan a sake gudanar da zabe a kasar.
A jawabin da Tebbun ya yi wa jama'ar kasar ya bayyana rushe majalisa, kuma za a sake gudanar da zabe da wuri, sannan cikin awanni 48 zai yi sauye-sauye a majalisar ministocinsa.