A tsakanin 7 da 8 ga Satumba za a gudanar da taron shawartar juna kan sha'anin siyasa tsakanin Turkiyya da Masar karo na 2 a Babban Birnin Ankara.
Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar ta bayyana cewa, za a gudanar da taron shawartar juna kan sha'anin siyasa tsakanin Turkiyya da Masar a karo na biyu karkashin jagorancin Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Jakada Sedat Onal da takwaransa na Masar Hamdi Loza.
Za a gudanar da taron a Ankara Babban Birnin Turkiyya a ranakun 7 da 8 ga Satumba, kuma za a tattauna game da alakar kasashen 2.