A ranar 13 ga watan maris za a gudanar da babbar zanga-zangar kin jinin gwamnati a Sanagal.
Sanarwar da Gamayyar Jam'iyyun Siyasa da Kungiyoyin Fararen Hula na M2D suka fitar ta ce, a ranar 13 ga Maris za a gudanar da zanga-zangar lumana a Dakar Babban Birnin Sanagal.
Sanarwar ta kuma ce, a ranar 12 ga Maris kuma, za a tuna da wadanda aka kashe a fadin kasar yayin gudanar da zanga-zanga.
An bayyana cewa, za a ci gaba da zanga-zangar har sai an saki dukkan magoya bayan madugun 'yan adawa Ousmane Sonko da ake tsare da su.
Sakamakon sakin Sonko da aka yi ya sanya aka soke znga-zangar da aka shirya yi a ranakun 8, 9 da 10 ga Maris.
A jawabin da Shugaban Kasar Sanagal Macky Sall ya yi, ya bukaci jama'ar kasar d su zauna lafiya.
Amma Sonko kuma ya ce za su ci gaba da fia kan titunan kasar.
Madugun 'yan adawar ya kara da cewa, an dade da fara juyin juya hali, babu wanda ya isa ya dakatar da hakan, kuma za su ci gaba da gwagwarmaya har sai sun kai juyin juya halin zuwa zaben shekarar 2024.