Sojojin da suka karbe mulki a Mali sun bayyana cewar hambararren Shugaban Kasar Ibrahim Boubacar Keita bai bukaci ya dawo kan kujerarsa ba, amma kuma za a ba shi damar zuwa duk inda yake so don a duba lafiyarsa.
Kakakin CNSP Mai gwagwarmayar kubutar da al'umma da suka yi juyin mulki kuma tun ranar 22 ga Agusta suke tattaunawa da tawagar ECOWAS da tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yake jagoranta, Isma'il Wague ya yi jawabi ga 'yan jaridu.
Ya ce za a kafa sabuwar gwamnati tsakanin sojoji da fararen hula a Mali, kuma ba gaskiya ba ne jita-jitar da ake yadawa ta za su zauna a kan mulki na tsawon shekaru 3, babu wanda ya fadi haka.
Wague ya sake jaddada cewar tare da dukkan jama'ar Mali za a tabbatar da mayar da mulki hannun farar hula.
An tambayi Wague cewar a lokacinda wakilan ECOWAS suka ziyarci Keita, shin ya nemi ya dawo kan mulki, sai ya bayar da amsa da cewar "Keita da kansa ya yi murabus kuma ya ce ba ya son ya dawo kan mulki. Yanzu abun da yake so shi ne a gaggauta mayarwa da farar hula mulki. Abun da jami'an suka bukata shi ne su ga Keita don su tattauna da shi, kuma mun ba su damar hakan. Wani abu kuma shi ne bukatar a tsare Keita a waje mai tsaro sannan a ba shi damar a duba lafiyarsa. An amince da wannan bukata. A duk lokacin da Keita yake so zai iya zuwa ko'ina don a duba lafiyarsa. Ya dawo a lokacin da yake so. ECOWAS sun tabbatar mana da zai dawo."
A ranar 18 ga Agusta ne wasu sojoji suka shiga Babban Birnin Mali inda suka kama Shugaban Kasar Keita tare da kai shi barikin soji na Kati. Da tsakar dare Keita ya sanar da ya yi murabus daga kan mulki.
Awanni kadan bayan murabus din Keita, sojoji 'yan juyin mulki sun sanar da cewar cikin kankanin lokaci za su gudanar da zabe a kasar.