Za a aiyana zaman makoki a Sanagal

Za a aiyana zaman makoki a Sanagal

A Sanagal za a aiyana zaman makoki sakamakon mutuwar mutane da dama zanga-zangar da ta barke a kasar bayan kama madugun 'yan adawa kuma shugaban jam'iyyar PASTEF Ousmane Sonko.

Sanarwar da aka fitar bayan taron Majalisar Ministoci ta ce, za a sanar da zaman makoki saboda wadanda suka mutu a ranakun 3 da 8 ga Maris, kuma za a sauke tutar kasar zuwa rabi.

Sanarwar ta jaddada yadda ake samun nasarar gangamin allurar riga-kafin Corona (Covid-19),  kuma a daren 19 ga Maris za a janye dokar ta baci kan kula da lafiya da aka sanya a Dakar da Thies a nanar 22 ga Janairu.

Sanagal ta sayi allurar riga-kafi ta Sinopharm daga China inda ta fara gangamin yin allurar a ranar 23 ga Fabrairu.

A karkashin shirin Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) na samun daidaito wajen rarraba allurar riga-kafin Corona a tsakanin kasashe matalauta, an aika da allurai dubu 324 na kamfanin AstraZeneca zuwa Sanagal a ranar 3 ga Maris.

Sanagal da ke da kusan mutane miliyan 10, ya zuwa yanzu mutane dubu 23 da 195 Corona ta kama a kasar. 935 daga ciki sun rasa rayukansu.


News Source:   ()