Hukumar kare yaduwar cututtuka ta Afirka ta bayyana cewa yawan wadanda ke dauke da kwayar cutar Corona a fadın nahiyar ya kai dubu 275,327.
Hukumar ta kara da cewa yawan wadanda suka rasa rayukansu a nahiyar sakamakon Coronar sun kai dubu 7,395 inda ta kara da cewa marasa lafiya dubu 125,316 sun warke.
Kasar Afirka ta Kudu ce keda mafi yawan masu dauke da Corona a nahiyar inda yawan yakai dubu 83,900 sai kuma Misira mai dubu 50,400.
Najeriya a yankin Afirka ta Yamma nada masu dauke da cutar dubu 18,500, Sudan a Afirka ta Gabas dubu 8,000 da Kamaru a Afirka ta Tsakiya nada dubu 10,100.
A yankin Kudancin Afirka an samu mutum dubu 87,900, a Afirka ta Arewa dubu 74,600, Afirka ta Yamma 57,300, Yankin Gabashin Afirka 29,300 sai tsakiyar Afirka 26,200.
Akallan marasa lafiya dubu 3,100 sun rasa rayukansu a yankin arewacin Afirka, 1,800 a Kudancin Afirka, 1,000 a yammaci sai kuma 883 a gabashi da kuma 571 a tsakiyar Afirka.