Yawan mace-macen zazzabin cizon sauro ya ragu zuwa matakan riga-kafin

Yawan mace-macen zazzabin cizon sauro ya ragu zuwa matakan riga-kafin

 

A cikin wani rahoto da ta fitar a yau Laraba,Hukumar lafiya ta Duniya ta yi kiyasin cewa mutane miliyan 263 ne suka kamu da cutar zazzabin cizon sauro a duniya a bara. Wannan na nuna ƙarin kusan mutane miliyan 11 idan aka kwatanta da 2022, aka kuma samu mutuwar mutane kusan 3,000.

Dangane da adadin mace-mace, “mun koma alkaluman kafin barkewar cutar”, Arnaud Le Menach, daga shirin zazzabin cizon sauro na duniya a hukumar lafiya, a wani y ana mai bayyana cewa a shekara ta  2020,barrazanar cutar Covid-19 ta haifar da karuwar mace-mace masu alaƙa da zazzabin cizon sauro, tare da ƙarin mutuwar 55,000.

Tun daga wannan lokacin, jimlar adadin mace-mace ya ragu sannu a hankali.

Ya kamata kuma a hanzarta yin rigakafin cutar don cimma damar raguwar cutar a Afirka, yankin da ya fi fama da cutar a duniya da kashi 94% na adadin masu kamuwa da cutar da kashi 95% na mace-macen da ke tattare da wannan cuta ta hanyar cizon sauro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)