A ranar Litinin kawai, shugaba Xi ya gana da shugabannnin ƙasashen Afrika ta Kudu, Guinea, Eritrea, Seychelles, Djibouti, Togo, Comoros, Mali Jamhuriyar Domikaradiyyar Congo, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran ƙasar, Xinhua ya ruwaito.
Ana sa ran wannan taron haɗin kai karo na 9, ya samar da wani tsarin da zai kasance abin koyi daga dangantakar China da ƙasashen nahiyar Afrika.
Taron na zuwa ne a daidai lokacin da ake cikin tankiya na siyasa a sassa dabam-dabam na duniya, inda za a ga yadda China za ta fifita matsayinta a dangantakarta da sauran manyan ƙasashe.
Daga cikin manyan maudu’an da za a tattauna da masu ruwa da tsaki a wannan taro akwai na cimma yarjejeniya kan yanayi da makamashi, da kuma batun haɗin kai ta fannin fasahar da sadarwar zamani.
A cikin shekarun da suka gabata, dangantaka tsakanin China, ƙasa mai tasowa mafi girma da Afrika, nahiyar da ke ƙunshe da mafi yawa daga cikin ƙasashe masu tasowa, ta na ci gaba da inganta, lamarin da ke zama misali na yadda ƙasashe za su yi hulda don haɓaka kansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI