Yau hukumar raya tafkin Chadi ke bude taron gwamnonin yankin karo na biyar

Yau hukumar raya tafkin Chadi ke bude taron gwamnonin yankin karo na biyar

Taron wanda ya haɗa ƙungiyoyin bayar da agaji, na ciki da waje, da gwamnoni takwas daga Najeriya da Kamaru, Chadi da kuma Jamhuriyar Nijar, zai mayar da hankali ne kan samar da mafita mai ɗorewa don inganta tsaro da zaman lafiya da ci gaba a ƙasashen dake kewaye da tafkin Tchadi.

Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Mai Mala Buni na jihar Yobe (mai masaukin baƙi), Babagana Umara Zulum na jihar Borno, Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa, Lidjima Abdraman na Hadjer-Lamis da Janar Saleh Haggar Tidjani na lardin Lac a Chadi, Brig. Janar Mohamadou Ibrahim na Diffa sai Midjiyawa Bakari na yankin Arewa mai Nisa da Abate Edi’i Jean na yankin Arewa, a ƙasar Kamaru.

Taron mai taken "Sake Gina Tafkin Chadi, Haɗin Kai kan Iyakoki da Tsaro”, na da zummar lalubo hanyoyin magance rashin zaman lafiya a yankin da kuma inganta haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen.

Mamman Nuhu, shugaban Hukumar raya tafkin Chadi, da rundunar haɗin gwiwa na ƙasashen yankin, ya ce taron ya samar da fili ga ƙungiyoyin agaji jin kai, da masu fafutukar neman zaman lafiya da masu ba da tallafi, tafka muhara domin neman mafita da ci gaban yankin.

Taron na zuwa ne daidai lokacin da mayakan Boko Haram da ISWAP suka zafafa hare-hare a ƙasashen yankin, kuma lokacin da Chadi ke barazanar ficewa daga ƙawancen yaƙi da ta’addanci a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)