Sashen ‘yan sanda na kasashe makwabta a Gabashin Afirka da suka hada da Sudan ta Kudu da Habasha sun cimma yarjejeniya a kan yaki da laifukan da ake aikatawa a kan iyakoki, musayar bayanan sirri da hadin gwiwa a fannin ilimi.
Kakakin ‘yan sandan Sudan ta Kudu, Daniel Justin ya bayyana cewar shugaban ‘yan sanda Majak Malik da takwaransa na Habasha, Demelash Gebremicheal sun sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa don kare tsaron kan iyaka a Juba.
Justin ya lura da cewa yarjejeniyar ta hada da musayar bayanan sirri, aiyukan kare iyakoki da kuma horar da ‘yan sandan Sudan ta Kudu a Habasha.