Jami’ar sadarwa da wayar da kan jama’a ta asusun na UNICEF Eva Hind ta bayyana cewa a cikin adadin da suka bayyana z a samu ƙananan yara sama da dubu ɗari 772 da ake hasashen matsalar yunwar za tafi ƙamari a kansu.
Dama dai wani rahoton wata cibiyar dake kula da sassan da fari ya addaba ta bayyanawa kamfanin dillanci labarai na AFP cewa tuni fari ya addabi wasu yankuna 5 a Sudan.
Ƙasar dai ta shafe watanni 20 ana gwabza yaki tsakanin sojojinta da dakarun ɗaukin gaggawa na RSF da suka kashe dubban mutane, yayin da majalisar ɗinkin duniya ta ce ƙasar Sudan ce kan gaba a yawan adadin ƴan gudun hijira a duniya.
Hind ta kuma tabbatarwa da cewa a halin yanzu ana sa ran yara miliyan 3 da dubu 200 za su fuskanci matsalar rashin abinci mai gina jiki.
Ta kuma ci gaba da cewa yawan yaran da ke fama da tamowa ya karu daga kimanin 730,000 a shekarar 2024 zuwa sama da 770,000 a shekarar 2025.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI