An bayyana cewa, yara kanana 'yan makarantar Islamiyya 136 aka yi garkuwa da su a yankin Tegina na jihar Niger da ke arewacin Najeriya a ranar 30 ga Mayu.
Mataimakin Gwamnan Jihar Niger Ahmed Ketso ya shaida cewa, sun tuntubi iyayen daliban da aka yi garkuwar da su inda suka tabbatar da adadinsu.
Ketso ya ce, "Za mu iya tabbatar da yara dalibai 136 aka yi garkuwa da su."
A ranar 30 ga Mayu ne 'yan bindiga suka kai hari kan makarantar Islamiyya ta Salisu Tanko da ke yankin Tegina na jihar Niger tare da yin garkuwa da da dalibai. Wani mutum 1 ya mutu sakamakon harin.
'Yan bindigar sun saki yara kanana 11 sakamakon yadda suka kasa yin tafiya.
'Yan bindigar sun kira malamin makarantar tare da neman a biya su kudin fansa har Naira miliyan 110 kafin su saki yaran.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira da a saki daliban ba tare da bata lokaci ba.