Daga karshe an baiwa danginta damar ziyartar ta.“Abin da muke da muka lura yanzu kam shi ne, tana cikin dammuwa kuma ta na mai fama da rashin lafiya,” in ji Ayachi Hammami, ɗaya daga cikin lauyoyinta. ‘Yar shekaru sama da 50 ta fara ne a tsakiyar watan Janairu don nuna rashin amincewa da tsare ta. Shugabar Hukumar Gaskiya da Mutunci da aka kafa bayan juyin juya halin Musulunci domin yin karin haske kan irin ta’asar da aka yi a tsawon shekarun mulkin kama-karya, ana zargin mai fafutuka da karya wani rahoto da kungiyar ta fitar.
Sihem Bensedrine, daya daga cikin mutanen da ake tsare da su a Tunisia © Fethi Belaid / AFP“Rahoton da ya fito bayan shafe shekaru hudu yana aiki da wannan hukuma ya kunyata kungiyoyin masu aikata ba dai dai ba da gudanar da zalunci daban-daban na gwamnatin Ben Ali. Ta yi imanin cewa wadannan hanyoyin sadarwa ne ke bayan abin da ke faruwa da ita a yanzu. Suna daukar ramuwar gayya ne saboda ta fallasa irin ta’asar da tsohuwar gwamnatin ta yi wa jama’a.
Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Duniya (FIDH) ta yi kira da a sake ta cikin gaggawa. Yosra Frawes, darektan ofishin Maghreb-Middle East na kungiyoyi masu zaman kansu ya ce "Muna daukar wannan a matsayin tsarewa ba bisa ka'ida ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI