WHO ta ce zuwa yanzu alluran rigakafin ƙyandar biri kusan miliyan guda aka rabawa ƙasashe 9 da cutar ta fi tsananta yayinda ake dakon wasu ƙarin tarin alluran a yaƙi da cutar mai haɗari.
WHO wadda ta ayyana dokar ta ɓaci kan cutar a watan Agustan shekarar nan, ta ce ƙyandar biri ta fi tsananta a ƙasashe 9 na Afrika da suka ƙunshi Jamhuriyar Congo mahaifar cutar kana Rwanda maƙwabciyarta da Cote d’Ivoire sannan Kenya da Liberia da kuma Nigeria baya ga Afrika ta kudu da Uganda kan jamhuriyar Afrika ta tsakiya.
WHO ta ce a Congo ne cutar ta fi tsananta inda ƙasar ke da kashi 4 bisa biyar na yawan masu ɗauke da cutar ta ƙyandar biri, dalilin da ya sanya a cewar hukumar aka fi karkatar da alluran rigakafin cutar zuwa ƙasar ta kudancin Afrika.
Cikin shekarar nan kaɗai ƙasashen Afrika 19 suka samu ɓullar cutar ƙyandar biri a wani yanayi da cutar ke ci gaba da yaɗuwa.
A Congo kaɗai mutum aƙalla dubu 38 ake tsammanin na ɗauke da wannan cuta yayinda ta hallaka mutane fiye da dubu guda.
Ƙasashe sun yi alƙawarin baiwa nahiyar ta Afrika alluran rigakafi fiye da miliyan 3 da dubu 600 don yaƙar cutar sai dai har kawo yanzu ƙasa da miliyan guda suka isa ga nahiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI