An yi gargadi game da yadda yanayin aiyukan jin kai a Somaliya ya kai matakin tabarbarewar mafi muni a watanni 6 da suka gabata.
Wakilin Musamman Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Adam Abdelmoula ya fitar da rubutacciyar sanarwar cewa, mata da yara kanana da suka gujewa rikici na iya fuskantar mummunan yanayin rashin kayan taimako.
Abdelmoula ya ce,
"A shekarar 2021 bukatar taimako ta karu amma a watanni 6 da suka gabata yanayin aiyukan jin kai a kasar ya kai mataki mafi muni."
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, akwai mutane miliyan 16 da ke bukatar taimakon gaggawa a SOmaliya, wasu mutanen miliyan 2,9 kuma sun bar matsugunansu.