Tun a ranar alhamis din da ta gabata rikicin ya fi karkata ne a yankin Sake mai tazarar kilomita ashirin daga yammacin Goma.
Cikin gaggawa,Shugaban Jamhuriyar DRCongo ya jagoranci majalisar tsaro a Kinshasa bayan da aka sanar da mutuwar gwamnan yankin Manjo Janar Peter Cirimwami, hafsa ne a rundunar sojojin sakamakon raunukan da ya samu.
Yan tawayen M23 sun kashe shi a ranar Alhamis, 23 ga watan Janairu, yayin da yake kan gaban daga da yammacin Goma. Ya samu rauni sosai, wanda duk da kokarin liktoci na ceto shi,said ai aka garzaya da shi a cikin daren Alhamis zuwa Juma'a zuwa Kinshasa.
Hukumomin kasar sun sanar da cewa "za a karrama gawar a Kinshasa," in ji Janar Ekenge.
Shugaban kasar Félix Tshisekedi, wanda ya dawo daga Davos na kasar Switzerland a yammacin ranar Alhamis, ya kira taron majalisar tsaro da ta maida hankali kan halin da ake ciki a yankin Goma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI