Ishasha dake kan iyaka da Uganda, shi ne gari na baya-bayan nan da ya fada hannun ‘yan kabilar Tutsi da ke samun goyon bayan kasar Rwanda. Kungiyar M23 ta kwace yankuna da dama a lardin Kivu ta Arewa na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo tun bayan da ta kaddamar da farmaki a karshen shekarar 2021.
Shugaban kungiyoyin farar hula Romy Sawasawa ya shaidawa AFP cewa "Ishasha ta fada hannun yan tawayen M23 ba tare da an fuskanci fad aba tsakanin dakarun M23 da sojojin DRCongo.
Wasu daga cikin mayakan M23 AFP - GLODY MURHABAZIRahotanni na bayyana cewa da kama garin ne yan sandan Congo suka tsallaka zuwa Uganda don cira da rayukansu ganin ta yda dakarun M23 suka shigo garin da tarin makamai.
Gad Rugaju, mataimakin jami'an tsaron Uganda a gundumar, ya tabbatar da cewa 'yan sandan Congo kusan 90 ne suka tsallaka zuwa cikin kasarsu.
Dakarun DRCongo AFP - ALEXIS HUGUETYa ce jami'an za su yi "kimantawa kuma za a iya korar su bayan an yi shawarwari". Kungiyar ta M23 ta kira taron inda suka shaida wa mutanen gari da su ci gaba da harkokinsu kamar yadda suka saba, kuma sun yi kira ga mayakan sa-kai da ke goyon bayan gwamnati da su hada kai su kuma ‘yan sanda su dawo, inji Yasini Mambo. Mambo ya kara da cewa, sun kuma gaya wa 'yan tawayen Hutu na Rwanda na jam'iyyar Democratic Forces for the Liberation of Rwanda (FDLR) da su koma gida Rwanda. Ishasha tana a kudancin tafkin Edward da ke da nisan kilomita 200 arewa maso gabashin Goma, babban birnin lardin Kivu ta Arewa.
Wasu daga cikin dakarun DRCongo a kotu REUTERS - Arlette BashiziKama garin na Ishasha na zuwa ne kwana guda bayan faduwar babban garin Nyamilima da ke kusa da shi, wanda mazauna yankin suka ce dakarun M23 ma sun karbe ba tare da gwabza fad aba.
Tsawon shekaru 30, yankin gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo mai arzikin ma'adinai ya sha fama da munanan fada tsakanin kungiyoyin masu dauke da makamai na cikin gida da na waje, tun daga yakin yankin na shekarun 1990.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI