Kungiyar ta AU mai dauke da kasashe 55,wannan mukamin an ware shi ne a wannan karo ga wakili daga gabashin Afirka. Wa'adin shugaban hukumar mai barin gado, dan kasar Chadi Moussa Faki Mahamat, zai kawo karshen wa’adinsa a watan Fabrairun 2025.
Kungiyar kasashen Afirka da ke da hedikwata a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, ta fitar da jerin sunayen 'yan takara hudu a jiya Laraba.
Tutocin kasashen Africa AFP - MICHELE SPATARIMahamoud Ali Youssouf, mai shekaru 58, ya tabbatar a watan Yuli yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP cewa, shine dan kawai dan takarar da zai iya daidaita tazarar da ke tsakanin yankuna daban-daban na Afirka, kasancewa mai jin Faransanci, amma kuma mai jin harshen Larabci.
Ministan Harkokin Waje na Djibouti Mahamoud Ali Youssouf daga Djibouti, karamar kasa ce a yankin kahon Afirka mai kusan mutane miliyan daya, ya karasa da cewa burinsa na farko idan aka zabe shi,shine kokarin kawo karshen yake-yake a nahiyar.
Shugabanin kasashen Afrika a taron kungiyar AU AFP - MICHELE SPATARIA wanan tafiya,yan takara kamar su Raila Odinga, mai shekaru 79, jigo a jam'iyyar adawa ta Kenya, wanda ya kuma nemi shugabancin kasar sau biyar ba tareda samun nasara ba,saitsohon ministan harkokin wajen Madagascar, Richard Randriamandrato, wanda ya mika takardar neman tsayawa takara a ranar Talata.
A watan Oktoban shekarar 2022 ne aka kore shi daga mukaminsa bayan da ya kada kuri'ar amincewa da kudurin Majalisar Dinkin Duniya wanda ya yi Allah wadai da mamayar da Rasha ta yi a Ukraine.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI