A kasar Ghana an fitar da sunayen mutanen da suka cancanci tsayawa takara a zaben watan disamba daga cikin ‘yan takara 24 da suka nuna shawa.
Mataimakin shugaba mai ci Mahamudu Bawumia ke kan gaba a jerin sunayen sanan tsofan Shugaban kasa kana Jagoran adawa John Dramani Mahama wanda ya mulki kasar daga shekara 2012 zuwa 2017 wanda kuri’a jin ra’ayin jama’a ta bayanna amatsayin wanda ka iya lashe zaben.
Sauran ‘yan takarar sun hada da tsohon ministan masana’antu Alan Kyerematen da kuma attajirin matashi Nana Kwame Bediako.
Hukumar zaben kasar Ghana ta bayyana soke takarar ragowa mutum 14 da tarin kura kuren da aka gano wajan harhada takardu, sai dai tuni ‘yan takarar da lamarin ya shafa suka kudiri anniyar qalubalantar matakin a gaban kotu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI