Yakubu wanda ya jagoranci tawagar masu sa ido daga hukumar zaben Najeriya, ya ce a kasar Ghana akwai siyasar akida inda 'yan siyasa kan kasance cikin jam'iyyarsu koda sun fadi zabe, sabanin yadda 'yan siyasar Najeriya ke yi.
Farfesa Yakubu ya yaba da dorewar dimokiradiyar Ghana da kuma yadda 'yan siyasa da magoya bayansu ke mutunta akidarsu da kuma zama cikin jam'iyya guda duk yanayin da suka samu kansu.
Shugaban hukumar zaben yace wannan shine dalilin da ya sa tsohon shugaban kasa John Dramani Mahama ya samu nasara, saboda jajircewarsa wajen takara a cikin jam'iyyarsa ba tare da sauya sheka ba.
Farfesa Yakubu ya kuma bayyana yadda hukumar zaben Ghana ta dauki tafarki irin na Najeriya wajen bayyana sakamakon zaben yan majalisu daga mazaba maimakon kai shi shelkwatar zabe na kasa baki daya.
Shugaban hukumar zaben Najeriya ya kuma yaba da yadda zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da samun tashin hankali ba, musamman yadda 'dan takarar jam'iyya mai mulki Mahmudu Bawumia ya fito fili ya taya abokin karawarsa murna ba tare da jiran bayyana sakamakon zaben ba.
Sakamakon zaben na Ghana ya nuna cewar tsohon shugaban kasa John Mahama ya samu nasara tare da kuma samun rinjaye a kujerun majalisar dokoki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI