'Yan sandan Kenya sun tarwatsa masu zanga-zanga yaki da cin zarafin mata

'Yan sandan Kenya sun tarwatsa masu zanga-zanga yaki da cin zarafin mata

.Akasarin masu zanga-zangar mata ne,inda suka yi tattaki daga babban birnin kasar Nairobi suna hura wusir tare da rera waken dake cewa ‘A bar kashe mata’yayin da a lokaci guda yan sanda cikin motocin su ke harba musu barkonun tsohuwa domin tarwatsa su.

Bugu da kari ,an gudanar da zanga-zangar a birane kamar Mombasa da Lodwar kamae yadda wadu faifan bidiyo keta zaga kafafen sadarwa.

Duk da an gudanar da zanga-zangar cikin lumana babu kwakkwarar hujja ko dalilin tarwatsa gangamin daga yan sanda,sai dai sun kama Babban Daraktan Amnesty Intyernational na kasar Irungu Houghton kamar yadda kungiyar ta sanar ciklin wani rahoto data fitar.

An dai gudanar da wannan zanga-zangar ne domin nuna adawa da kisan mata da ya yawaita a kasar,inda a tsakanin watan Agusta zuwa octoban wannan shekarar da muke ciki a kalla mata 97 ne aka kashe a lokuta daban-daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)