Bayanan da ke zuwa daga ƙasar da kuma wasu faya-fayan bidiyo da aka wallafa a Facebook sun nuna yadda jami’an ƴan sanda suka yi amfani da ƙarfi kan masu zanga-zangar ta hanyar harbin iska da kuma harba borkono tsohuwa kan dandazon jama’a da kai ga tarwatsa mutane.
Mutum guda ne dai ya samu mummunan rauni a wannan arangama ko da ya ke akwai wasu da dama da suka galabaita sakamakon bugun da jami’an tsaron suka musu.
Tun a ranar 9 ga watan nan aka kaɗa ƙuri’a a zaben na Mozambique wanda ɗan takarar jam’iyyar adawar ƙasar Venancio Mondlane ya sha alwashin jagorantar zanga-zangar ƙasa baki ɗaya don ƙalubalantar sakamakon bayan da suka yi zargin cewa jam’iyya mai mulki ta Frelimo na amfani da salon maguɗi wajen ci gaban da kasancewa a karagar mulki.
Duk da cewa sai a ranar 24 ga watan nan ne cikakken sakamakon zaɓen na Mozambique zai fita, amma sakamakon yankuna ya nuna yadda Frelimo ta lashe kashi 66 batun da ke nuna yiwuwar jam’iyyar ta ɗora kan mulkin shekaru 49 da ta shafe ta na yi a ƙasar.
Jam’iyyar dai ita ce ɗaya tilo da ke mulkin Mozambique tun bayan samun ƴanci daga Portugal
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI