‘Yan majalisu 84 sun goyi bayan gwamnatin rikon kwarya a Libiya

‘Yan majalisu 84 sun goyi bayan gwamnatin rikon kwarya a Libiya

‘Yan majalisu 84 daga yankunan Tobruk da Tripoli sun bayyana goyon bayansu ga gwamnatin rikon kwaryar da aka kafa a kasar.

Sun bayyana cewa “Mu ‘yan majalisun wakilai da muka rabata hannu  akan wacannan takardan muna kira ga takwarorinmu da su amince da gwamnatin rikon kwarya da kuma ba ta damar da za ta kafa hukumra samar da zaman lafiya a kasar”

Sanarwar kuma ta yi kira ga sabon firaiministan kasar Abdul Hamid Dbeibah da ya kafa gwamnatin hadin gwiwa akan “kwarewa, gaskiya da iya aiki”

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Libiya Jan Kubis ya tattauan da Dbeibah ta wayar tarho akan matakan kafa gwamnati a kasar.


News Source:   ()